Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
TikTok ya maka gwamnatin Amurka a gaban kuliya
2020-08-25 10:28:12        cri
A jiya ne kamfanin yada bidiyo na kasar Sin "TikTok", ya shigar da gwamnatin Donald Trump na kasar Amurka kara, kan umarnin da ya bayar na haramtawa duk wani Ba-Amurke yin mu'amala da uwar kamfanin wato ByteDance.

A cikin wani kundin bayani mai shafuka 39, wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe, an sanya sunayen shugaba Donlad Trump na Amurka, da sakataren harkokin cinikayya Willbur Ross da sashen cinikayya na Amurka cikin wadanda ake kara.

A cewar kundin, TikTok ya zargi, hukumomin Amurka da tauyewa kamfanin hakkinsa ba tare da gabatar da wasu kwararan shaidu, da za su tabbatar da daukar wannan mummunan mataki ba, da bayar da wancan umarni ba tare da bin matakan da suka dace ba, kamar yadda doka ta biyar da aka yiwa gyaran fuska ta tanada, yayin da aka haramtawa kamfanin gudanar da harkokinsu ba tare da an ba shi wani wa'adi ko wata dama ta kare kansa ba.

A halin da ake ciki dai, kundin ya gabatar da kalaman da shugaba Trump ya furta, kan wannan batu, kamar ikirarin da ya yi a taron yakin neman zabensa cewa, TikTok, ba shi da "iko" kuma zai haramta amfani da manhajar da ta shahara, idan har kamfanin bai biya gwamnatin kudi neman amincewar sayar da shi ba. Wadannan kalaman sun sabawa doka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China