Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Putin na neman dawo da huldar Rasha da Amurka a fannin tsaron bayanai
2020-09-26 16:19:07        cri
A cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na Shugaban Rasha Vladimir Putin a jiya, Rasha na neman dawo da cikakkiyar dangantaka tsakaninta da Amurka, a fannin tsaron bayanai. Sanarwar ta ce barazanar fito-na-fito a fannin fasahar zamani muhimmiya ce dake gaban al'ummar duniya a yanzu, kuma masu ruwa da tsaki a bangaren, na da rawar takawa wajen hana aukuwar fito-na-fiton.

Shugaba Putin ya ce, ya kamata Rasha da Amurka su dawo da tattaunawar manyan jami'ai a kai a kai, tsakanin hukumomin kasashen masu ruwa da tsaki a bangaren tsaron bayanai na kasa da kasa da kuma mara baya ga tattaunawa da dangantaka tsakanin hukumomin a fannonin da suka shafi tunkarar masu kutse da tabbatar da tsaron kasa da rage hadarin nukiliya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China