Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Rasha tana son hada kai da kasar Sin a fannin fasahar 5G
2020-08-24 10:00:56        cri
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya bayyana cewa, kasarsa tana sha'awar yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannin fasahar 5G.

Ministan wanda ya bayyana haka yayin taron dandalin Ilimi na dukkan matasan Rasha mai suna "Territory of Meanings", ya ce, kasarsa ba za ta yi koyi da Amurka ba, wadda kullum take hana kowa yin mu'amula da kasar Sin kan fasahar 5G, musamman kamfanin Huawei.

Lavrov ya kara da cewa, sabanin matakin na Amurka, Rasha tana son yin mu'amula da sauran kasashe, ta yadda za a hada kai wajen samar da fasahohi na zamani, a kuma aiwayar da su a zahiri.

A cewarsa, yanzu haka, sassa da hukumomin da abin ya shafa, sun himmatu wajen raba fasahar 5G a kasar Rasha, Yana mai cewa, fasahar 5G, wani muhimmin al'amari ga Rasha da kuma duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China