Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi Jinping ya fadawa duniya tunaninsa na gina tsarin al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama
2020-09-20 20:40:47        cri
Kwanaki kadan da suka shude, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai karbi goron gayyatar halartar babban taron murnar cika shekaru 75 da kafuwar MDD, kuma zai gabatar da muhimmin jawabi ta kafar bidiyo.

A shekaru da dama, shugaba Xi Jinping ya sha fayyace bayanai game da manufar gina tsarin al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bin adama a lokutan da ya halarci manyan tarukan kasa da kasa, inda ya sha nanatawa duniya cewa, al'ummar Sinawa suna da muradin yin aiki tare da jama'a daga dukkan sassan kasashen duniya domin gina ingantaccen muhallin rayuwa ga daukacin al'ummar duniya.

A lokacin da ya halarci muhawara a babban taron MDD karo na 70 a shekarar 2015, Xi Jinping ya sha nanata cewa zaman lafiya, ci gaba, adalci, demokaradiyya, da 'yanci, su ne muhimman ginshikan dake shafar daukacin bil adama kuma su ne manyan kudurorin MDD. A duniyar da muke a yau, dukkannin kasashen duniya suna damfare da junansu ne, suna musayar dadi da wuya tare. Ya kamata dukkan bangarori su rungumi tsare-tsaren manufofin MDD, su yi kokarin gina sabon tsarin huldar kasa da kasa mai cike da manufar cin moriyar juna, kuma a yi kokarin gina tsarin al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.

Shekaru biyu daga bisani, shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi mai taken, "Mu hada gwiwar gina tsarin al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil adama" wanda ya gabatar a helkwatar MDD dake birnin Geneva. Haka zalika, ya taba jaddada cewa: "Ya kamata kasashen duniya su gina tsarin hadin gwiwar tattaunawa, ba tare da yin fito-na-fito ba, kuma su yi huldar ba tada jijiyar wuya ba. Ya kamata manyan kasashe su girmama muhimman bukatu da moriyar junansu, su magance rikice-rikice, da kawar da banbance-banbance a tsakaninsu, su sa himma da kwazo wajen gina sabuwar duniya mai cike da zaman lafiya, ba tare da tsokanar juna ba, su girmama juna, da kulla dangantakar moriya ga kowane bangare."

"Bai kamata a ja da baya daga bakin daga da zarar an fuskanci wahalhalu ba." Domin yin cikakken bayani game da manufar samar da tsarin al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama, Xi Jinping ya sha nanata cewa, tilas ne mu samar da yanayin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, a yi musayar damammaki da moriya mai salon bude kofa, kuma a yi kokarin cimma nasarar kafa tsarin hadin gwiwa wanda zai samar da sakamako na moriyar juna. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China