Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Kasar Sin Ya Karfafa Gwiwar Matasa Da Su Yi Amfani Da Lokacinsu
2020-09-18 14:18:08        cri

Jiya Alhamis 17 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki a kwalejin Yuelu a jami'ar Hunan. Lokacin da yake barin kwalejin, dalibai da malamai sun taru domin yi masa gaisuwa, tare da yin Shewa da tafi.

Kwalejin Yuelu yana daya daga cikin manyan kwalejoji guda 4 na kasar Sin masu dogon tarihi, wanda aka gina a shekarar 976 bayan haihuwar Annabi Isa A.S. Kana daya daga cikin dadaddun kwalejojin da har yanzu ake tafiyar da harkokin ba da ilmi a tarihin ba da ilmi mai zurfi na duniya. Haka kuma shi ne sansanin kasar Sin na kirkiro tunani da sabunta ilmi.

A yayin da yake kwalejin, shugaban kasar Sin ya gaya wa dalibai cewa, yanzu lokaci ne na jarumai, don haka wajibi ne matasa su ba da gudummawa wajen farfado da al'ummar Sinawa bisa kaifin basirarsu. Ya kuma karfafawa matasa gwiwa da kada su bata lokacin kuruciyarsu, su fito da daidaiton ra'ayin yadda suke kallo da ma rayuwa a duniya, su dauki mataki na farko yadda ya kamata a rayukansu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China