Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jagoranci taron shugabannin Sin da Jamus da Turai
2020-09-15 10:00:25        cri
Shugabannin kasashen Sin da Jamus, da mambobin kungiyar tarayyar Turai ta EU, sun amince su kara karfafa tattaunawa da hadin gwiwa, don tabbatar da nasarar muhimman ajandojin siyasa da aka sa gaba tsakanin Sin da EU, da kara zurfafa amincewa da juna, da neman cimma moriyar juna, da inganta cudanyar sassa daban daban, da kara daga darajar alakar sassan zuwa matsayi na gaba.

Sassan sun amince da hakan ne, a yayin taron da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi hadin gwiwar jagoranta daga nan birnin Beijing, a jiya Litinin ta kafar bidiyo. Sauran jagororin taron sun hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda kasar ta ke rike da shugabancin karba karba na kungiyar EU, da kuma shugaban majalissar Turai Charles Michel, tare da jagoran hukumar zartaswa ta Turai Ursula von der Leyen.

Cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya bayyana cewa, cutar COVID-19 ta zaburar da wani babban sauyi da mai yiwuwa sau daya zai wakana a karni, lamarin da ya sake sada daukacin al'ummun duniya a wani sabon yanayi na bukatar juna.

Shugaba Xi ya ce, yana da muhimmanci Sin da EU su tsaya tsayin daka wajen samar da ci gaba madaidaici a bangarorin hadin gwiwar su bisa matsayin koli daga dukkanin fannoni, su kuma martaba ka'idoji hudu, da suka hada da wanzar da yanayi na zaman lumana, da gudanar da komai a bayyane, da hadin gwiwa, da cudanyar sassa daban daban, da tattaunawa da kuma jin ta bakin juna.

Har ila yau shugaban na Sin, ya bukaci shigar da nahiyar Afirka cikin tsarin sassa uku, don martaba bukatun nahiyar, yana mai fatan sassan kasa da kasa, musamman cibiyoyin hada hadar kudi na kasa da kasa, da masu samar da lamuni, za su kara azama wajen saukewa kasashen Afirka basukan da ke wuyansu.

A daya bangaren kuma, shugaba Xi ya yi karin haske game da matsayin kasar sa, don gane da batutuwan da suka shafi yankunan musamman na Hong Kong, da jihar Xinjiang, yana mai cewa matakan da babban yankin Sin ke dauka game da su, na da nasaba ne da tsaron kasa da ikon mulkin kai, da hadin kan kasa, da kare 'yancin daukacin al'ummu daban daban dake rayuwa da aiki a yankunan. Ya ce Sin na matukar adawa da dukkanin wani mutum ko kasa, dake fatan haifar da rashin zaman lafiya, da rarrabuwar kawuna, da tashin hankali a yankunan ta, da ma masu yunkurin tsoma baki cikin harkokin gidan kasar.

Daga nan sai shugaba Xi ya bayyana cewa, ba wata hanyar gudanarwa da ta fi ko wacce ta fuskar wanzar da ci gaba, illa dai wadda ta fi dama dama. Don haka kamata ya yi kasashen duniya su dukufa wajen warware nasu matsaloli. Kuma Sinawa ba za su amince da karbar umarni daga wani ba, ta fakewa da batun 'yancin dan Adam ko mulkin danniya, da yin bakin ganga. Kaza lika Sin a shirye ta ke, ta karfafa musaya da kasashen Turai, bisa manufar martaba juna, ta yadda sassan biyu za su samu irin ci gaban da suke fata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China