![]() |
|
2020-09-20 16:38:33 cri |
Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce, shi da shugaba Bhandari sun kaiwa juna ziyara a kasashensu a bara, inda aka samu kyautatuwar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Nepal, zuwa wani matsayi na tabbatar da kulla zumunta daga zuriya zuwa wata, don neman ci gaban kasashen da kyautatuwar zaman rayuwar al'ummominsu, gami da hadin gwiwa a fannonin wasu manyan tsare-tsare. Sa'an nan a wannan shekarar da muke ciki, kasashen 2 sun kara karfafa zumuncinsu, bisa hadin kansu a kokarin dakile cutar COVID-19. A cewar shugaba Xi, yana dora matukar muhimmanci kan aikin raya huldar dake tsakanin kasashen 2, kana zai yi kokari tare da shugaba Bhandari na kasar Nepal, don neman samun ci gaban ayyukan kyautata hulda da hadin gwiwa a fannoni daban daban, domin samar da alfanu ga kasashen 2, da jama'arsu. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China