Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta baiwa Sudan ta kudu tallafin gaggawa na hatsi
2020-09-18 10:48:16        cri
An yi bikin mika tallafin gaggawa na hantsi da Sin ta baiwa kasar Sudan ta kudu, a jiya Alhamis a birnin Juba, helkwatar kasar.

Yayin bikin, minista mai kula da harkokin jin kai da daidaita bala'u Peter Mayen Majongdit, a madadin gwamnati da jama'ar Sudan ta kudu, ya nuna godiya ga taimakon da Sin take baiwa kasarsa a kan lokaci. Ya ce, Sin ta dade tana samarwa Sudan ta kudu taimakon jin kai, kuma tana kokarin tallafawa kasar wajen gina manyan ababen more rayuwa, da ma samar da tallafin jinyya, kuma matakan da Sin take dauka, na goyon bayan bunkasuwar kasar cikin lumana. Ya kuma yi fatan kasashen biyu za su kara hadin gwiwa nan gaba don kawo alheri ga jama'ar su.

Shugaban kwamitin magance bala'u da samun farfadowa na Sudan ta kudu Manasseh Lomole, ya ce Sin ta ba da tallafi a kan lokaci a wannan karo, zai kuma taimakawa jama'ar kasar tinkarar mawuyacin hali.

Jakadan Sin dake kasar Hua Ning ya nuna cewa, a halin yanzu ana fuskantar raguwar farashin mai da ma cutar COVID-19, da dai sauraun bala'u daga indallahi, abubuwan da suka jefa kasar cikin hadari na jin kai, inda fiye da rabin mutane suna fama da karancin hatsi. A daya hannun gwamnatin Sin da jama'arta, na mai da hankali kan lamarin, da ba da taimako gwargwadon karfinta, matakin da ya fitar da jama'ar kasar daga mawuyacin hali mai tsanani. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China