Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta kudu ta dora alhakin karayar tattalin arzikinta kan rikici da cutar COVID-19
2020-09-12 16:26:21        cri
A jiya Juma'a kasar Sudan ta kudu ta bayyana cewa, matsalar tashe tashen hankula da yaduwar annobar COVID-19 su ne musabbabin karyewar tattalin arzikin kasar.

Salvatore Garang Mabiordit, ministan kudi da tsara tattalin arzikin kasar, ya ce rikice rikice a tsakanin kabilun kasar, da bala'u daga indallahi, da kwararar farin dango, da rashin tabbas a kasuwannin mai na duniya, su ne suka yi sanadiyyar durkushewar tattalin arzikin kasar.

Yace rashin ingantaccen tsarin tattara kudaden harajin kasar shi ma ya taimaka wajen gurgunta yunkurin farfado da tattalin arzikin kasar.

A watan Agusta, Sudan ta kudu ta bayyana neman bashin dala miliyan 250 daga bankin shigi da fici na Afrika, domin tallafawa tattalin arzikin kasar daga komadar da ya samu a sakamakon annobar COVID-19.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China