Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kauyen Shazhou Da Shugaba Xi Ya Kaiwa Ziyara
2020-09-17 10:51:41        cri

A jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a kauyen Shazhou dake lardin Hunan na kasar, inda ya gane ma idonsa yadda ake gudanar da ayyukan rage talauci a wurin.

Kauyen Shazhou ya kasance a wani yankin duwatsu, inda fadinsa ya kai muraba'in kilomita 0.92. Gaba daya mutane 529 ne ke zaune a cikin kauyen, kana 340 daga cikinsu 'yan kabilar Yao ne.

Yanzu haka a cikin kauyen, ana kokarin raya harkar yawon shakatawa, don taimakawa rage talauci. Ban da wannan kuma, 'yan kauyen suna dasa itatuwa masu samar da 'ya'ya, da gudanar da kwas don horar da fasahohi masu alaka da sana'o'i daban daban, irinsu girki, da aikin yawon shakatawa. Ta wannan hanya 'yan kauyen fiye da 350, sun samu ayyukan yi, gami da karin kudin shiga.

A lokacin baya, akwai matalauta 95 a cikin kauyen. Zuwa shekarar 2018, an samu kawar da talauci gaba daya a kauyen. Sa'an nan zuwa karshen shekarar 2019, yawan kudin shiga na duk shekara ga mutum daya a kauyen, ya kai Yuan 13,840, kwatankwacin dalar Amurka 2,049. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China