Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fitar da sakamakon binciken adadin yawan alummar Xinjiang
2020-09-15 10:35:40        cri

Wani masani dake aiki a jami'ar Xinjiang farfesa Lin Fangfei, ya fitar da sakamakon bincike da ya gudanar, game da yawan al'ummar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta.

Rahoton binciken na farfesa Lin, mai taken "Martani ga karairayin Adrian Zenz game da kayyade iyali a Xinjiang: bincike game da damar haihuwa ga matan kananan kabilu na jihar Xinjiang," wanda aka wallafa a jiya Litinin, ya soki karairayi, da jita jita da ake yadawa game da yawan al'ummar dake zaune a jihar Xinjiang.

A cewar sakamakon binciken na farfesa Lin, jita jitar cewa wai, ana tilasawa matan Xinjiang daina haihuwa, karya ce tsagwaronta, kuma labarai ne marasa tushe da wasu kafafe, da masana na Amurka da kawayen ta na yammacin duniya ke kitsawa.

Ya ce ko shakka babu, akwai shaidu dake nuna raguwar karin hayayyafa a Xinjiang, to sai dai kuma ko alama, hakan ba shi da nasaba da hana haihuwa kamar yadda Adrian Zenz, da wasu masana, da gwamnatocin wasu kasashe yamma ke zargi.

Ya ce babban dalilin raguwar yawan al'umma a yankin, na da nasaba ne da dadaddiyar manufar Sin ta cimma nasarar bukasawa, da inganta rayuwar mata da kananan yara. Kasancewar Xinjiang na yankin kudanci, yankin na samun ci gaban zamantakewa da tattalin arziki cikin sauri. Kuma karin mata daga kananan kabilun jihar na cin gajiya daga damar samun ilimi, da aikin yi, suna kuma samun karin 'yanci, ko zabi game da hayayyafa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China