Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da goyon bayan MDD ta fuskar kawar da talauci
2020-09-17 10:36:56        cri

A Jiya Laraba ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu, ya yi jawabi a gun taron da jaridar People's Daily ta gabatar ta kafar bidiyo, mai taken "Sin da MDD: Kawar da talauci da samun zaman lafiya da bunkasuwa tare".

Ma ya nuna cewa, cutar COVID-19 na ci gaba da addabar kasashen duniya, har ta sa tattalin arzikin duniya na samun koma baya mai tsanani, lamarin da ya sa al'ummun duniya kimanin miliyan 70 zuwa 100 na fuskantar barazanar fadawa kangin talauci. Don haka a cewar jami'in. kamata ya yi, duniya ta nacewa tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da goyon bayan MDD ta yadda za ta taka rawarta, da ingiza raya kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya.

Ma, ya kuma kara da cewa, Sin ta mai da aikin kawar da talauci a matsayin wani abu mai muhimmanci na gudanar da harkokin kasa. A bana kasar Sin na ci gaba da yaki da talauci duk da bullowar cutar, har ma za a kai ga cimma nasarar kawar da talauci shekaru 10 kafin lokacin da aka tsayar, karkashin ajandar samun bunkasuwa mai dorewa zuwa shekarar 2030.

Kaza lika, Ma ya ce, Sin za ta tabbatar da matakan da shugaba Xi Jinping ya sanar, a gun babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa karo na 73 a dukkanin fannoni, tare kuma da goyon bayan kasashe musamman ma maso tasowa, ta yadda za su yaki da cutar, da farfado da tattalin arziki da zaman al'ummarsu, da kuma cika alkawarin da Sin ta dauka, na samar da allurar rigakafi ga kasashe daban-daban. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China