Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Laimar kwadi ta taimakawa manoman gundumar Fuping wajen kawar da talauci
2020-09-07 14:33:21        cri

A ran 29 ga watan Faburairun bana, gundumar Fuping ta lardin Hebei ta fita daga jerin gundumomin kasar Sin dake fama da kangin talauci, wannan ya alamta cewa, a hukumance an cire "Matsalar kangin talauci" daga gundumar. Wani dalilin da ya sa gundumar Fuping ta samu nasarar kawar da talauci shi ne ta yi kokarin raya sana'ar noman laimar kwadi. A tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019, yawan kudin da gundumar ta samu daga sana'ar noman laimar kwadi ya kai kusan RMB yuan biliyan 1, yawan kudin shiga da kowane magidanci da ya noma laimar kwadi ya samu, ya karu fiye da Yuan dubu 10. Sakamakon haka, ma iya cewa, laimar kwadi ta kasance tamkar wani tsiro dake taimakawa manoman gundumar Fuping wajen kawar da talauci da kuma samun arziki.

A yayin ziyarar da wakilinmu ya kai, ya ga matashi Zhang Qiang, mai shekaru 23 da haihuwa yana aiki a cikin gonarsa ta laimar kwadi. Bana shekara ta biyu ke nan da ya koma garinsu ya fara noman laimar kwadi. Zhang Qiang, wanda ya taba koyon fasahar gyara motoci a birnin Beijing, ya koma garinsu domin kulawa da mahaifiyarsa wadda ba ta da lafiya. Gurbin aiki na farko da ya samu a garinsu shi ne kulawa da laimar kwadi da aka noma a wani yanki, inda ake da dimbin manyan gonakin noma laimar kwadi. Bayan da ya ga sauran manoma da suka samu wadata sabo da noman laimar kwadi, hakan ya karfafa masa gwiwar noman laimar kwadi, kana ya samu rancen kudi RMB Yuan dubu 100 daga banki, ya kuma yi hayar wasu manyan gonaki biyu domin noman laimar kwadi. Bisa manufar tallafin gwamnatin wurin, yawan kudin ruwa da ya kamata ya biya cikin shekaru 3 bai kai kudi RMB yuan dubu 10 ba.

"Na samu rancen kudi RMB Yuan dubu 100, ya kamata in mayar wa banki wadannan kudi da kudin ruwa cikin shekaru 3. Amma idan har ban mayar da su cikin lokaci ba, za a iya tsawaita lokaci. A bara, na yi hayar manyan gidaje biyu domin noman laimar kwadi, na samu kudin RMB Yuan wajen dubu 90, tattalin arzikina ya karu, na iya kara abubuwa."

A lokacin da yake bayyana yawan kudin shiga da ya samu a bara, Zhang Qiang yana mai cewa, bai taba samun kudi da yawa kamar haka ba. Zhang Qiang ya kara da cewa, a cikin manyan gidaje biyu da ya yi haya, ya noma laimar kwadi na yau da kullum ne kawai. A lokacin sanyi, ba zai iya noman laimar kwadi a ciki ba sakamakon matukar sanyi. Bisa shirinsa, Zhang Qiang ya ce, yana son yin hayar karin wasu manyan gidaje biyu, inda zai noman laimar kwadi a lokacin sanyi.

A da, ba a san sana'ar noman laimar kwadi a gundumar Fuping ba, amma yanzu ta samu bunkasuwa sosai. Kawo yanzu, an gina manyan gidaje na noman laimar kwadi dubu 4 a yankunan musamman na raya sana'ar 98. A shekarar 2019, wadannan manyan gidaje sun taimakawa magidanta fiye da dubu 7 wajen kawar da talauci. An yi hasashen cewa, ya zuwa karshen shekarar da muke ciki, yawan kudin da za a iya samu daga sana'ar noman laimar kwadi a gundumar Fuping zai kai fiye da RMB Yuan biliyan 2.5, wato sana'ar za ta iya taimakawa dukkan magidanta wadanda suke fama da talauci, sannan yawan kudin shiga da kowane magidanci zai samu zai karu zuwa fiye da RMB Yuan dubu 20. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China