Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar tallafin ba da jiyya ta taimakawa manoma da makiyaya na kabilar Tibet
2020-09-15 11:18:37        cri

A shekarun baya bayan nan, manoma da makiyaya na gundumar Xinghai na yankin kabilar Tibet mai cin gashin kanta dake lardin Qinghai, sun ci gajiyar aikin likitancin gargajiya na kabilar Tibet, saboda manufar tallafin ta ba da jiyya da gwamnatin ke aiwatarwa a yankin, matakin da ya kara inganta tsarin kiwon lafiyar jama'ar wurin, ba tare da biyan kudade da yawa ba.

Likitancin gargajiya na kabilar Tibet, wata alama ce ga gundumar Xinghai, wanda ya samu karbuwa matuka daga manoma da makiyaya a wurin. A shekarar 2009, aka kafa asibitin likitancin gajiya na kabilar Tibet, inda mazauna wuri suke iya samun jiyya cikin sauki, ko da yake akwai wuyar sauya tunanin makiyaya na samun jiyya a lokacin da suke da ciwo mai tsanani.

Masu aikin jiyya na asibitin, su kan kai ziyara a kauyuka daban-daban na tsawo wata daya ko biyu a ko wace shekara, don samar da magunguna ga mazauna kyauta, da yada ilmin kandagarkin annoba, da kiwon lafiya da dai sauransu.

Ban da wannan kuma, hanya mafi dacewa da ta baiwa manoma da makiyaya damar samun jiyya ita ce, rage kudaden da za su biya wajen samun jiyya, karkashin manufar rangwame da gwamnati ke bayarwa.

Ya zuwa yanzu, ba jama'ar gundumar asibitin ke ba su jiyya kadai ba, har ma jama'ar gundumomi ko birane a kewayen su, suna iya samun jiyya a wurin. Shugaban asibitin Zhou Latai ya ce, nagartacciyar manufar da gwamnatin ke dauka, ta baiwa asibitinsa damar kiyaye lafiyar jikin manoma da makiyaya a wuri. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China