Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da kamfanonin Sin 100,000 sun taimakawa shirin kawar da talauci
2020-09-14 11:26:42        cri

Ya zuwa watan Yuni, kimanin kamfanoni masu zaman kansu 109,500 ne suka shiga ayyukan shirin yaki da fatara a kauyukan da suka fi fama da talauci a kasar Sin, babban jami'in hukumar kula da dukkan kamfanoni da masana'antun cinikin kasar Sin ACFIC ya bayyana hakan.

Wadannan kamfanonin masu zaman kansu sun taimakawa kauyuka 127,100, wanda ya kunshi kauyuka 68,900 da aka yiwa rejista a matsayin wadanda suka fi fama da talauci, Fan Youshan, mataimakin shugaban hukumar ACFIC, ya fadawa taron dandalin da aka gudanar a yankin Danzhai dake shiyyar kudu maso yammacin lardin Guizhou.

Wadannan kamfanoni masu zaman kansu sun samar da kusan kudin Sin RMB Yuan biliyan 91.6 kwatankwacin dala biliyan 13.4 na jarin kamfanoni da aka zuba a yankunan da suke fama da talaucin a shekarun da suka gabata, inda aka samu karin Yuan biliyan 15.2 na ayyukan kyautata walwalar jama'a.

Kamfanonin sun taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi 799,000 kana sun horar da mutane 1.16, kana mutane masu fama da talaucin da suka yi rejista ya kai miliyan 15.64.

Hukumar ta ACFIC za ta jagoranci kamfanoni masu zaman kansu domin samar da karin kudade wanda zai amfani kauyuka sama da 1,100 da har yanzu ba su fita daga kangin fatara ba don taimakawa shirin gwamnatin kasar Sin na yaki da talauci. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China