Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda aka kawar da talauci a kauyen Shuanghong
2020-09-09 15:52:11        cri

Kauyen Shuanghong yana garin Daduan na gundumar Tonggu dake birnin Yichun na lardin Jiangxi na kasar Sin, adadin mutane masu fama da talauci a wannan kauye shi ne mafi yawa a gundumar Tonggu. Ko da yake, babu gonaki masu yawa, amma, kauyen na da albarkatun iccen gora.

Wannan ya sa, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta birnin Yichun ta tsara shirin musamman, tare da tura wakilai, da darektan JKS, da tawagar taimakawa masu fama da talauci zuwa kauyen, domin taimakawa kauyen Shuanghong kafa wata masana'antar sarrafa iccen gora, inda za a iya sarrafa iccen gora da nauyinsu ya kai kilogiram miliyan 1. Lamarin da ya ba da gudummawa matuka wajen fitar da kauyen Shuanghong daga kangin talauci.

Shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa, babbar dabarar kawar da talauci ita ce habaka sana'o'i. Ya kamata mu habaka sana'o'i iri daban daban bisa halayen da sassan kasar suke ciki, domin kawar da su daga talauci ta hanyoyin da za su dace.

Tun lokacin da aka kafa masana'antar sarrafa iccen gora a kauyen Shuanghong a shekarar 2019, ya zuwa yanzu, zaman rayuwar manoman kauyen ya kyautata sosai, kuma, wannan aiki ya kara kudin shiga na mazauna kauyen baki daya, ta yadda ya kara tabbaci wajen kiyaye masu fama da talauci, da samar da kudade wajen gina ababen more rayuwa a wannan kauye. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China