Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe ta kara yawan sa'o'in kasuwanci bayan bude tattalin arzikinta a yaki da cutar COVID-19
2020-09-15 11:22:20        cri
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta sanar a ranar Litinin cewa, ta kara yawan sa'o'in gudanar da kasuwanci yayin da kasar ke cigaba da bude harkokin tattalin arziki sannu a hankalin, yayin da ake tsaka da yaki da annobar COVID-19.

Ministar yada labaran Zimbabwe, Monica Mutsvangwa ta ce, a yanzu lokutan kasuwanci na kananan 'yan kasuwa, da manyan diloli, da masu ayyukan hidima, wanda ake gudanarwa daga karfe 8 na safe zuwa 4:30 na yamma, an tsawaita shi inda za'a fara kasuwancin daga karfe 6:30 na safe zuwa 6:30 na yamma ba tare da bata lokaci ba.

Mutsvangwa ta ce, a yayin da suke bude harkokin tattalin arzikin kasar sannu a hankali, suna yin hakan ne bayan daukar dukkan matakan kariya da suka dace domin yaki da wannan cutar abokiyar gaba, wato COVID-19.

Ta ce, sassauta dokar kullen ba ya nufin alamun kawo karshen cutar ba ne, sai dai yana gwada cewa, kasar tana kokarin daidaita bukatun tattalin arzikinta da kuma bukatar tabbatar da kare rayukan al'ummarta. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China