Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar jamian lafiya na kasar Sin ta isa Zimbabwe domin taimakawa yaki da COVID 19
2020-05-12 10:35:04        cri

 

Tawagar jami'an lafiya na kasar Sin ta isa Zimbabwe a jiya Litinin, domin taimakawa kokarin kasar ta yankin kudancin Afrika, yaki da annobar numfashi ta COVID-19.

Tawagar mai kunshe da jami'ai 12 daga lardin Hunan na kuma dauke da kayayyakin lafiya, ciki har da na'urar taimakon numfashi da kayayyakin gwaji da makarin hanci da baki da rigunan kariya.

Tawagar ta kunshi kwararru a sashen kula da numashi da na cututtuka masu yaduwa da sashen kula da marasa lafiya masu tsanani da likitancin gargajiya na kasar Sin da na sashen dakile yaduwar cututtuka da kula da lafiyar al'umma da kuma aikin jinya.

 

 

Jami'an za su gabatarwa takwarorinsu na Zimbabwe gogewar da suke da shi a fannin dakile annobar da kuma horar da su kan matakan kariya da dakilewa da aikin duba marasa lafiya da jinyarsu.

Da yake jawabi yayin da yake tarbarsu a filin jirgin saman kasa da kasa na Robert Mugabe dake birnin Harare, Jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun, ya bayyana godiya ga gwamnatin lardin Hunan da asibitocin dake lardin, bisa tura jami'an zuwa Zimbabwe. Ya kuma godewa dukkan likitocin tawagar bisa zuwa Zimbabwe domin yaki da cutar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China