Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a bude asibitin yaki da COVID-19 mai salon kasar Sin irinsa na farko a kasar Zimbabwe
2020-07-23 11:44:08        cri
Cibiyar Health Point Upper East Medical Center, wani asibiti ne irinsa na farko a kasar Zimbabwe wanda zai dinga gudanar da aiki bisa ma'aunin kasar Sin, kuma za'a bude asibitin a yau 23 ga wata domin fara karbar majinyata masu fama da cutar COVID-19.

A halin yanzu asibitin yana da sama da ma'aikatan lafiya 50, da gadaje 50, ana sa ran za'a kara adadin gadajen zuwa 80 a nan gaba. A asibitin, na'urorin kiwon lafiya kamar na'urar dake taimakawa numfashi da makamantasu duk an yi odarsu ne daga kasar Sin. Baya ga haka, kwararrun likitocin kasar Sin masu aikin agaji suna bada horo ga ma'aikatan lafiyar kasar ta Zimbabwe.

A cewar Michael Li, shugaban asibitin na Health Point Upper East Medical Center, wasu kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu uku dake Tianjin ne suka kafa asibitin tare da hadin gwiwar wani kamfanin samar da hidimomin kiwon lafiya na kasar Zimbabwe mai suna Health Point, inda suka zuba jarin dala miliyan 3. A matakin farko, za'a fara amfani da asibitin wajen jinyar masu fama da cutar COVID-19, daga bisani za'a mayar dashi zuwa asibitin kwararru bayan kawo karshen annobar COVID-19.

Daraktan cibiyar Health Point yace, yana fatan asibitin zai warkar da karin majinyata masu fama da cutar COVID-19, kuma tsarin da za'a yi amfani da shi na salon kasar Sin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China