Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe ta karbi gudummuwar kayayyakin yaki da COVID-19 daga hamshakin dan kasuwar kasar Sin, Jack Ma
2020-03-25 09:44:59        cri
Yayin da aka samu mutane 3 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Zimbabwe, kasar ta karbi gudunmuwar kayayyakin da za su taimaka mata yaki da cutar, daga hannun hamshakin dan kasuwar kasar Sin wato Jack Ma.

Kayayyakin da Zimbabwe ta karba a jiya Talata, wani bangare ne na gudunmuwar da tsohon shugaba kuma daya daga cikin wadanda suka kafa rukunin kamfanin Alibaba wato Jack Ma, ya bayar ga kasashen Afrika. Inda ya bada su ta hannun Tarayyar Afrika (AU).

Kayayyakin sun hada da kayayyakin gwaji 20,000 da makarin baki da hanci 100,000 da rigunan kariya da makarin fuska guda 1,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China