![]() |
|
2020-08-28 14:07:57 cri |
Ya ce, tsarin mulkin kasar Sin ya nuna cewa, dukkanin al'ummomin kasar Sin suna da 'yancin bin addini, kuma jihar Xinjiang ta tsara manufofin dake shafar 'yancin addini, ana kiyaye aikace-aikacen addinai bisa dokoki, kuma ba wani mutum ko wata kungiya, da za su iya tsoma baki cikin wadannan harkoki.
Cikin taron, shugaban ofishin sarrafa albarkatun kwadago, da tabbacin zaman al'umma na jihar Xinjiang, Rehemanjiang Dawuti, ya bayyana cewa, zargin wai ana tilastawa al'ummomin jihar yin aiki, labari ne na jabu, wanda wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya suka kirkira.
A nasa bangare kuwa, shugaban ofishin ba da ilmi na jihar Parhati Izmu, ya ce ba a taba tilastawa dalibai zama a makarantu ba, kuma labaran da kafofin watsa labaran kasar Amurka suka fidda, cewar, wai tsarin ba da ilmi, tare da tilastawa dalibai zama a makarantu na jihar Xinjiang, ya raba yara da iyayensu, wannan labari karya ce kawai, wadda aka tsara domin bata sunan kasar Sin. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China