Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang na kara farfadowa bayan shan fama da cutar COVID-19
2020-09-03 10:56:12        cri

Ya zuwa karshen ranar Talata 1 ga watan nan na Satumba, ba a sake samun mutum ko guda da ya harbu da cutar numfashi ta COVID-19 a jihar Xinjiang ta kasar Sin ba. Hakan ya nuna cewa, jihar ta kubuta daga sabbin masu harbuwa da cutar tsawon kwanaki 15 a jere.

Rahotanni sun ce, an gudanar da matakan kandagarki da shawo kan cutar a dukkanin yankunan jihar, kana matakan da aka aiwatar na kare rayukan daukacin al'ummun yankin, sun sa yanayin rayuwa na yau da kullum na ci gaba da komawa kamar da.

A 'yan kwanakin baya bayan nan, birnin Urumqi ya aiwatar da matakan kashe kwayoyin cuta a wuraren da jama'a ke amfani da su, da sashen sufuri na al'umma. Kaza lika fannin sufurin jihar ya farfado, inda motocin haya na tasi ke kara fadada ayyukan su sannu a hankali, yayin da wuraren shakatawa na al'umma, da na bude ido suka sake budewa.

A gabar da ake kara tunkarar lokacin kwararar masu yawon bude ido zuwa jihar ta Xinjiang, hukumar raya al'adu da yawon bude ido ta Xinjiang ta sanar da cewa, tun daga ranar 2 da watan nan, aka fara bude mafiya yawan wuraren da masu yawon shakatawa ke halarta, yayin da tuni aka amince da ci gaba da harkokin yawon bude ido tsakanin larduna da birane.

Tun daga farkon ranar 15 ga watan Yuni zuwa karshen ranar 1 ga watan Satumbar nan, jinhar Xinjiang ta tabbatar da warkewar mutane 804, bayan da suka harbu da cutar, yayin da kuma aka sallami wasu mutanen su 229, da suka harbu da cutar amma ba su nuna alamun ta ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China