Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Filin jirgin saman kasa da kasa na Urumqi zai fara jigilar fasinja zuwa wajen jahar Xinjiang a watan Satumba
2020-08-30 17:21:39        cri

Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanonin jiragen sama masu yawa za su dauki tsauraran matakan kandagarkin annobar COVID-19, yayin da filin jiragen saman kasa da kasa na Urumqi zai fara jigilar fasinja daga watan Satumba.

Daga ranar 1 ga watan Satumba, reshen kamfanin jiragen sama na China Southern Airlines a jahar Xinjiang zai dawo da zirga-zirga daga birnin Urumqi zuwa Lanzhou, Guangzhou, Hangzhou, Changsha, Xiamen, Tianjin da sauran wurare, inda za'a fara sauka da tashin jiragen sau daya a kowace rana a matsayin farawa.

Tun daga ranar 29 ga watan Agusta, an sassauta matakin barazanar annobar COVID-19 a gundumomin Tianshan da Shaybak dake yankin Urumqi, daga matakin babban hadari zuwa matakin karamin hadari. Matakin hadari na yankin ci gaban tattalin arziki da fasaha na Urumqi a gundumar Toutunhe, za a sassauta shi daga matsakaici zuwa karami. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China