Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Tanzania da Uganda sun cimma matsayar gina bututun mai
2020-09-14 09:43:17        cri
Shugaban kasar Tanzania John Magufuli, da takwaransa na kasar Ugandan Yoweri Museveni sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin shimfida bututun man fetur na dala biliyan 3.5.

Yarjejeniyar, an kulla ta ne a asalin kauyen shugaba Magufuli, wato garin Chato dake arewa maso yammacin kasar Tanzania a ranar Lahadi, lamarin da ya ba da damar ci gaba da aikin shimfida bututun man mai tazarar kilomita 1,445 inda za a dinga tura man daga rijiyoyin man kasar Uganda dake yankin Hoima zuwa tashar ruwan Tanga a kasar Tanzania.

Shugabannin kasashen biyu sun bukaci jami'an kasashen biyu da su gaggauta kammala dukkan tsare-tsaren da suka dace domin fara aikin.

Kasar Uganda ta fara hako albarkatun mai ne a shekarar 2006, kasar tana da gangar danyen mai sama da biliyan 6.5. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China