Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tanzania ta ba da umarnin kwashe mutane 25,000 don kaucewa hadarin tumbatsar madatsar ruwa
2020-02-17 11:57:39        cri
Mahukuntan kasar Tanzania a gundunar arewacin Mwanga sun bayar da umarnin kwashe mutane kimanin 25,000 dake zaune a wasu kauyuka dake daura da madatsar ruwa ta Nyumba ya Mungu domin mayar da su yankunan mafiya tsaro don gujewa fuskantar tumbatsar madatsar ruwan da ake fargabar faruwarsa sakamakon mamakon ruwan sama da aka shekawa a yankin.

Kwamitin bayar da kariya da tsaron madatsar ruwan Mwanga dake shiyyar Kilimanjaro ya sanar cewa idan har mazauna yankunan suka ki amincewa a kwashe su daga yankunan dake daura da madatsar ruwan, hukumomi za su tura 'yan sanda don su kori mazauna kauyukan da karfin ikonsu.

An yi kiyasin kusan masunta 3,500 ne ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin a tsakanin mazauna kauyukan kimanin 25,000 wadanda suka kafa kauyuka 26 na masu kamun kifi dake kewaye da madatsar ruwan.

Philip Patrick, wani masanin albarkatun ruwa daga ofishin kula da tafkin Pangani ya ce, hukumomi a yankunan Kilimanjaro, Simanjaro da Manyara da suke amfani da madatsar ruwan an riga an ba su gargadi game da yiwuwar tunbatsar madatsar ruwan. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China