Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF ta yabawa Tanzania game da yadda ta saukaka tsarin rajistar haihuwar yara
2020-08-11 12:06:47        cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF), ya yabawa sabon tsarin da kasar Tanzania ta bullo da shi wajen saukaka tsarin yin rajistar haihuwa ga yara 'yan kasa da shekaru biyar, a cewar UNICEF, tsarin zai taimakawa yara masu yawa a kasar wajen neman hakkokinsu da kuma samun kariya.

Rene Van Dongen, wakilin hukumar UNICEF a Tanzania ya ce, takardar shaidar haihuwa wata muhimmiyar takarda ce dake tabbatar da haihuwar yaro.

Jami'in na UNICEF ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da sabon tsarin saukaka yin rajistar haihuwar yara a shiyyoyin Tanga da Kilimanjaro, inda ake sa ran yi wa yara 'yan kasa da shekaru biyar sama da dubu 580 rajistar haihuwar nan da watanni biyu masu zuwa.

Tanga da Kilimanjaro, sun shiga sahun shiyyoyin kasar 16 inda aka yiwa yara 'yan kasa da shekaru biyar sama da miliyan 4.6 rajistar haihuwar tun bayan kaddamar da shirin a shekarar 2013.

Sabon tsarin ya haifar da samun karuwar rajistar haihuwa ga yara 'yan kasa da shekaru biyar a wadannan shiyyoyi na kasar daga kasa da kashi 10 bisa 100 zuwa sama da kashi 80 bisa 100.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China