Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tanzania za ta gayyaci kamfanonin kasashen waje domin aikin shimfida layin dogon da zai hada kasar da Rwanda da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
2020-03-02 10:23:21        cri
Gwamnatin Tanzania, ta ce ta na dab da gayyatar kamfanonin kasashen waje domin aikin gina layin dogon, daga tashar kan tudu ta Isaka, zuwa kasashen Rwanda da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo dake makwabtaka da kasar.

A cewar kakakin gwamnatin kasar, kuma babban sakataren ma'aikatar yada labarai, Hassan Abbasi, nan bada dadewa ba za a sanar da kamfanonmnin da za su yi aikin.

Ya bayyana yayin wani taron manema labarai jiya a birnin Dodoma cewa, shugaban kasar John Magafuli, ya riga ya bada umarnin gina layin dogon da zai hada kasar da makwabtan kasashen 2.

Ya kara da cewa, aikin ginin layin dogon da ya tashi daga Dar es Salaam, babban birnin kasuwanci na kasar, zuwa Morogoro, mai kilomita 200 ya kai kaso 75, yana mai cewa ginin layin dogo daga Morogoro zuwa Makutopora a Dodoma kuma, ya kai kaso 28.

Har ila yau, ya ce manyan sakatarori daga ma'aikatun kasar, za su shafe kwanaki 2 cikin wannan makon wajen nazarin ci gaban da aka samu dangane da ginin layin dogon. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China