Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya zai samar da bashin dala miliyan 446 ga Tanzania domin yaki da fatara
2020-02-18 11:24:28        cri

Shugaban asusun yaki da fatara na kasar Tanzania ko TASAF a takaice, Mr. Ladislaus Mwamanga, ya ce bankin duniya ya alkawarta samarwa kasar tallafin bashin kudade da yawan su ya kai kudin kasar shilling tiriliyan 1.03, kwatankwashin dalar Amurka miliyan 445.92, domin aiwatar da matakan kasar na yaki da talauci.

Mr. Mwamanga ya ce a cikin shekaru 5 masu zuwa, za a kashe kudi da yawan su ya kai shillings tiriliyan 2, wato kusan dalar Amurka miliyan 865.87, a zango na 2 na ayyukan da ke gudana, karkashin asusun na TASAF, wanda tuni shugaban kasar John Magufuli ya kaddamar a birnin Dar es Salaam cibiyar kasuwancin kasar.

Jami'in wanda ya bayyana hakan, yayin wata tattaunawa da gidan talabijin mallakar kasar ya watsa, ya ce Tanzania za ta nemo sauran kudaden da ake bukata ne daga sauran sassan na abokan huldar ta, ciki hadda asusun kungiyar OPEC na raya kasa da kasa, wanda ya alkawarta baiwa kasar dala miliyan 50. Mr. Mwamanga ya kara da cewa, shirin na da nufin baiwa magidanta damar shiga sassan sana'o'i daban daban, wadanda za su rika samar masu da kudaden shiga.

Tun da fari yayin kaddamar da shirin, shugaba Magufuli ya ba da umarni ga dukkanin sassan hukumin gwamnati dake larduna da gundumonin kasar, da su sanya ido kan yadda ake aiwatar da kashi na biyu na shirin TASAF, ta yadda manufar gwamnatin mai ci ta yaki da tsananin talauci zai yi nasara, tsakanin 'yan kasar dake cikin mawuyacin hali. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China