Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rayuwar Ma Guocai Mai kiwon shanu na jihar Ningxia ta kyautata zaman rayuwarsa
2020-09-11 17:11:51        cri

Ma Guocai, mai shekaru 37 dan kabilar Hui ta jihar Ningxia a baya ya yi fama da talauci, kudin da yake samu a waje bayan ya bar kauyensu, ba shi da yawa. A shekaru 5 da suka gabata, ya amsa kiran gwamnatin kauyensa, da ya koma gida ya kuma fita daga talauci har ma rayuwarsa ta inganta.

Ma Guocai ya zauna a kauyen Hantianling dake garin Hexi na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, wannan kauye ne da mutane da dama suka kaura zuwa wurin suke zaune. A shekarar 2014 ne, Ma Guocai ya kaura zuwa kauyen, da farko ya koyi kiwon rago tare da mazauna kauyen, amma ba da jimawa ba, wata annoba ta bulla. Saboda rashin kwarewa, sama da raguna 100 sun mutu a sakamakon cutar. Don haka, baya ga hasarar kudin shiga da ya yi, ya kuma kara karbar basussuka.

Sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta Sin dake kauyen Hantianling Ding Jianhua ya kware kiwon shanu, don haka ya taimakawa Ma Guocai sosai. Haka kuma ya taimakawa Ma Guocai ya samu shanu 17 ta hanyar tsaya masa, saboda ba shi da kudi, bayan kiwon su na tsawon watanni 4 ya kuma sayar da su, ya samu ribar da ta kai Yuan fiye da dubu 30.

Bayan shekara guda, Ma Guocai yana da shanu fiye da 10, ya kuma biya dukkan basussukan da ake binsa a karshen shekarar. Ga Ma Guocai, yana iya samun kudin shiga fiye da Yuan dubu 200 cikin sauki a shekara guda. A karshen shekarar bara, ya gabatar da rokonsa na cire shi daga sunaye masu fama da talauci, ta yadda sauran 'yan uwansa mazauna kauyen za su iya samun albarkatun da ake bukata na fita daga kangin talauci. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China