Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalibai Dake Taimakawa Wajen Raya Kauyuka
2020-09-10 16:12:54        cri

A yayin da hasken rana ya ratsa rumfunan noman itacen Passion Fruit a safiya, mutanen kauyen Gaobu dake lardin Jiangxi na kasar Sin sun fara shiryawa don fara aiki. A nasu bangare kuma, wasu matasa sun bar gida, sun kama hanyar zuwa cibiyar samar da 'ya'yan itatuwa na Passion Fruit, don taimakawa aikin tsintar 'ya'yan itatuwan.

Cikin wadannan matasan, wasunsu na karatu a jami'a a cikin manyan birane, sa'an nan sun yi amfani da lokacin hutunsu don taimakawa aikin rage talauci a kauyensu. Wasu kuma sun riga sun gama karatun jami'a, amma sun koma kauyensu inda suka kama aiki a matsayin jami'ai masu kula da aikin kawar da talauci. Yayin da saura kuma sun koma kauyen ne don gudanar da aikin kasuwanci.

Ji Zhixiong, shi ne babban jami'i mai kula da aikin rage talauci na kauyen Gaobu, wanda ya ce, "Daliban kauyuka su kan nemi shiga birane. Amma a kauyen Gaobu, ana samun daliban da suka dawo gida, don taimakawa aikin kawar da talauci, da raya kauyen. "

Dawowar wadannan matasa kauyen, ya ba kauyen damar samun sabon tunani, da fasahohi, ta yadda ake kyautata zaton samun karin ci gaban kauyen a nan gaba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China