Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abokai, Wadanne abubuwa ku ka shirya yi a shekaru biyar masu zuwa?
2020-09-10 11:27:47        cri
Abokammu, me ku ka shiri yi da ma fatanku a shekaru biyar masu zuwa, wato daga shekarar 2021 zuwa shekarar 2025?

A nan kasar Sin, gwamnati ta tsara wani sabon shirin raya kasa cikin shekaru biyar masu zuwa, yanzu haka, tana neman shawarwari kan wannan shiri.

A don haka, muna gayyatar ku, ku kulla alkawari na shekaru biyar da kasar Sin. Muna kuma son ku amsa mana wasu tambayoyi. Mun gode!

1. Cikin shekaru 5 masu zuwa, Shin, kuna da sha'awar zuwa yawon shakatawa, ko yin karatu, ko kuma aiki a kasar Sin?

A. E.

B. A'a.

2. Shin, a halin yanzu kuna amfani da wasu na'urorin kirar kasar Sin?

A. Haka ne. Kamar tufafi, takalma, na'urorin wutar lantarki, wayar salula, manhaja da sauransu.

B. Babu.

3. Ko kun taba kallon fina-finan kasar Sin?

A. E.

B. A'a.

4. Kuna da masaniya cewa fasahar 5G ta kasar Sin tana kan gaba a duniya?

A. Na sani.

B. Ban sani ba.

5. Ko Kun san shawarar "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar?

A. Na sani.

B. Ban sani ba.

6. Ko kun san tsarin hidimar taswira mai yin amfani da taurarin dan Adam na Beidou na kasar Sin?

A. Na sani.

B. Ban sani ba.

7. Ko kuna da imani kan cewar kasar Sin za ta cika alkawarinta na samar wa duniya allurar rigakafin cutar COVID-19, bayan ta yi nasarar nazarin allurar?

A.E, ina da imani.

B.A'a, ban yarda ba.

8. A ganinka, cikin shekaru biyar masu zuwa, yaya yanayin kasuwancin kasar Sin zai kasance?

A. Zai karu.

B. Zai ragu.

9. Mene ne ra'ayinku game da jarin da kasar Sin ta zuba a kasarku?

A. Ina maraba.

B. Ba na so.

10. A ganinku, yaya dangantakar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin kasarku da kasar Sin za ta kasance cikin shekaru 5 masu zuwa?

A. Za ta inganta.

B. Za ta lalace.

11. Mene ne abun da ci gaban kasar Sin zai kawo wa duniya?

A. Kyakkyawar dama.

B. Kalubale.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China