Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bayyana kudirinta na aiki da abokan huldarta don kara karfin SCO na tunkarar hadurra
2020-09-11 09:40:43        cri
Mamban majalisar gudanarwra kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana kudirin kasarsa na yin aiki kafada da kafada da abokan huldarta, don kara karfin kungiyar hadin hadin ta Shanghai (SCO) na tunkarar duk wasu hadurra da kalubale da ka iya kunno kai yadda ya kamata.

Ministan Wang wanda ya bayyana haka jiya Alhamis, yayin taron majalisar ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar, Ya kuma gabatar da shawarwari guda biyar, kan yadda za a karfafa hadin gwiwa karkashin laimar kungiyar.

Na farko,Ya kamata mambobin kungiyar, su goyi baya da kuma kare muradun juna. A cewarsa, har yanzu makiya daga ketare na ci gaba na tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe mambobin kungiyar, kuma wannan na daga cikin kalubale guda da dukkan kasashe mambobin kungiyar suke fuskanta

Na biyu, ya kamata kasashe mambobin SCO, su ci gaba da hada kai, da yin hadin gwiwa, domin yakar cutar COVID-19. Yana mai cewa, a shirye kasar Sin take ta zurfafa hadin gwiwa da dukkan sassan a yaki da wannan annoba, da ci gaba da bunkasa matakan kandagarki da hana yaduwar cutar a kan iyakokin kasashe, da ba da muhimmanci ga bukatun kasashe mambobin SCO, bayan da kasar Sin ta yi nasarar samarwa da ma fara amfani da alluran riga kafin cutar numfashi ta COVID-19.

Na uku, ya kamata kasashe mambobin SCO, su ci gaba da musayar muhimman bayanai, don kawo karshen matsalolin tsaro daban-daban da ake fuskanta. Wang ya ce, ya kamata mu rika amfani da nagartaccen tsarin tsaro na bai daya kuma mai dorewa, don jure matsin lamba daga kungiyar 'yan ta'addan gabashin Turkistan da sauran tashe-tashen hankula da ayyukan 'yan ta'adda, da maganin abin da ya kira "makiya uku" daga amfani da cutar Covid-19 wajen haddasa rudani.

Na hudu, Ya kamata kungiyar SCO ta nace ga tsarin samun cigaba da matakan farfado da tattalin arziki a kasashe mambobin kungiyar, da daidata matakan dakile tasirin annobar, da yadda suke raya tattalin arziki, da karfafa tsara manufofi a fannin kananan sana'o'I da daidata dabarun ci gaba, da samar da hanyoyin musayar jami'ai cikin sauki da sufurin manyan hajoji ba tare da gurbata muhalli ba,da tabbatar da kwanciyar hankali da yin takara a fannin masana'antu da samar da kayayyaki a shiyya, da ci gaba da inganta harkokin ciniyayya da zuba jari, da bunkasa shawarar ziri daya da hanya daya cikin inganci bisa manyan tsare-tsare.

Na biyar. Ya kamata SCO ta nace ga hadin gwiwar bangarori daban-daban, da inganta yadda ake tafiyar da harkokin kasa da kasa. Ministan ya kara da cewa, kasashe mambobin kungiyar, sun cimma matsaya cewa, ya kamata a kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD da tsari da dokokin kasa da kasa.

Daga karshe Wang, ya ce, martaba hadin gwiwar sassa daban-daban, ya zama tushen tsayawar kasa da kafafunta, musamman galibin kanana da matsakaitan kasashe na duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China