Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Morocco ta tarwatsa maboyar kungiyar IS, ta damke mayaka 5
2020-09-11 14:52:02        cri

Hukumar tsaron kasar Morocco ta sanar cewa, ta tarwatsa maboyar mayaka masu da'awar kafa daular musulunci ta IS, ta kuma cafke mutane 5 daga mayakan kungiyar.

A wata sanarwar da hukumar binciken kasar Morocco ta fitar ta ce, an gudanar da aikin sintiri ne babu kakkautawa a biranen Tangier, Tiflet, Temara da Skhirat, lamarin da ya yi sanadiyyar kama mutanen da ake zargin biyar 'yan tsakanin shekaru 29 zuwa 43.

Biyu daga cikin mutanen da ake zargin an kama su ne a birnin Tiflet, mai tazarar kilomita 80 daga babban birnin kasar Rabat, da kuma birnin Temara dake yankin gundumar birnin Rabat.

A lokacin sintirin, an gano abubuwan fashewa uku, da manyan wukake da takubba, da wasu sinadarai da kuma sinadarin ammonium nitrate mai nauyin kilogram uku.

Sanarwar ta ce, binciken farko ya gano cewa, mayakan suna shirin kaddamar da hari ne a wasu muhimman wuraren kasar Morocco ta hanyar amfani da abubuwan fashewa.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China