Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Morocco za ta karbi bakuncin taro na 4, kan tsaro na nahiyar Afrika
2019-10-08 14:13:28        cri
Morocco za ta karbi bakuncin taron tsaro na Afrika karo na 4, a Rabat, babban birnin kasar, daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Disamban bana, mai taken " tasirin sauyin yanayi kan tsaro a nahiyar Afrika".

Wata sanarwa da Cibiyar bincike ta Atlantis, wadda kuma ke shiryar taron ta fitar, ta ce taron zai mayar da hankali kan batutuwa 3 da suka hada da wadatar abinci da samar da ruwa, da karuwar jama'a da raya aikin gona da kuma hasashen makomar nahiyar.

Sanarwar ta ce Sama da manyan jami'ai 400 daga kasashen 66 za su halarci taron, ciki har da Ministoci da jami'an gwamnati da masu ruwa da tsaki kan tasirin sauyin yanayi a kan tsaro a Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China