![]() |
|
2020-07-10 10:24:02 cri |
Yayin wani taron manema labarai, kakakin gwamnatin kasar, Saaid Amzazi, ya ce matakin da aka ayyana a fadin kasar, zai tsawaita har zuwa 10 ga watan Augusta, a matsayin wani bangare na yaki da annobar COVID-19.
Morocco ta bada rahoton samun sabbin mutane 308 da suka kamu da cutar a ranar Alhamis, wanda ya kawo jimilar wadanda suka kamu da cutar a kasar ta arewacin Afrika zuwa 15,079, ciki har da mutane 242 da suka mutu.
Kasar ta Morocco ta kuma fara sassauta matakan kulle na yaki da COVID-19. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China