Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Morocco ta cafke 'yan ci rani ta barauniyar hanya har 27,317
2019-12-26 11:11:06        cri

'Yan sandan kasar Moroco, sun gabatar da rahoton shekara a jiya Laraba, wanda ke cewa, a shekarar nan da muke ciki, an samu nasarar cafke 'yan ci rani ta barauniyar hanya da yawansu ya kai 27,317, ciki hadda 'yan kasashen ketare 20,141.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito alkaluman da 'yan sanda suka bayar jiya, inda suka ce a shekarar 2019, an kawar da kungiyar masu fataucin mutane 62, kuma an cafke mutane 505 masu alaka da wannan mugun aiki.

Labarin ya kara da cewa, an gano wasu takardun bogi, na ba da izni ga yawon bude ido a ketare, ko takardun shaida a hannun wasu mutane 3,021 da aka kama.

Rahotanni na cewa, a halin yanzu Morocco ta zama daya daga wurare na yada zango ga 'yan Afrika, dake son tafiya Turai domin neman rayuwa mafi kyau. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China