![]() |
|
2019-12-21 15:39:45 cri |
Taron na kwanaki uku, wanda kungiyoyin daliban kasashen Afrika tare da hadin gwiwar hukumar al'amurran kasa da kasa ta kasar Morocco suka shirya, wanda ya samu halartar kungiyoyin dalibai da kungiyoyin matasa wadanda ba na gwamnati ba har ma da wasu kungiyoyin matasa na shiyya da na kasa da kasa.
Da yake jawabin bude taron, ministan harkokin wajen kasar Morocco, Nasser Bourita, ya ce ya zama tilas kasashen Afrika su kara kaimi wajen yin hadin gwiwa don bunkasa harkokin ilmi, da samar da horo da guraben ayyukan yi.
Ya kara da cewa, ya kamata kasashen su kara azama wajen tabbatar da bunkasa ci gaban ilmi, da ba da horo da kuma samar da ayyukan dogaro da kai ga matasa. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China