Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin kula da asusun raya zaman lafiya da ci gaba na Sin da MDD ya gudanar da zamansa karo na biyar
2020-09-11 10:05:44        cri
A jiya ne, kwamitin dake kula da asusun raya zaman lafiya da ci gaba na Sin da MDD, ya gudanar da taronsa karo biyar ta kafar bidiyo. Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, da darekta a ofishin mataimakiyar babban sakataren MDD Maria Luiza Ribeiro Viotti da sauran mambobin kwamitin na FUND na daga cikin mahalarta taron.

A jawabinsa jakada Zhang ya ce, a cikin shekaru biyar da kafuwar asusun, kasar Sin ta zuba kudaden da suka kai dala miliyan 100 da taimakawa ayyuka sama da 80, wadanda suka amfani kasashe masu tasowa da dama, a yankin Asiya da Afirka da Latin Amurka da Oceania.

Ya kara da cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta yi amfani da asusun, a matsayin wani dandali na zurfafa hadin gwiwa da sakatariyar majalisar, da kare hadin gwiwar bangarorin daban-daban, da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama.

Sakatariyar MDD ta bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa asusun zuwa wannan lokci, asusun yana ci gaba da goyon MDD wajen jagorantar ayyukan tabbatar da zaman lafiya a duniya, matakin da ya kara nuna goyon baya ga MDD a kokarin da take na tunkarar kalubalen zaman lafiya da ci gaba da duniya take fuskanta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China