Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi watsi da zargin da Amurka da Birtaniya ke yi kan batun Xinjiang
2020-08-25 10:01:19        cri

Jakadan kasar Sin a MDD a ranar Litinin ya yi watsi da zarge-zargen da wakilan kasashen Amurka da Birtaniya ke yiwa jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin da cewa ba su da tushe kuma karya ne tsagwaronta.

Geng Shuang, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya ce, "Kasar Sin ta yi watsi da zarge-zargen da wadanann wakilai na kwamitin sulhun MDD ke yi. Ya ce, ba su da tushe kuma karya ce da suka saba yinta".

Halin da ake ciki a jihar Xinjiang batu ne na cikin gidan kasar Sin. Ba batu ne na addini ko hakkin dan adam ba. Sai dai, batu ne da ya shafi yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, in ji Geng. "Ta'addanci abokin gaba ne ga kowa. Babu wani batu mai kyau a cikin ayyukan 'yan ta'adda. Kasar Sin tana Allah wadai kuma tana cikakken goyon bayan yaki da ta'addanci.

Jihar Xinjiang ta sha fuskantar ayyukan ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayin addini a shekarun baya. Domin magance wadannan barazana, Xinjiang ta dauki jerin matakan yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayin addini. Wannan ya yi daidai da yarjejeniyar kwamitin sulhun MDD, karkashin ajandar yaki da ta'addanci na kasa da kasa na MDD, don kawar da ayyukan tsattsauran ra'ayin addini, wakilin na Sin ya bayyana hakan ne a taron kwamitin sulhun MDD ta kafar bidiyo game da batun barazanar zaman lafiya da tsaro da ake fuskanta a duniya sakamakon ayyukan ta'addanci. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China