Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhu MDD ya amince da kudirin dokar shigar da mata ayyukan wanzar da zaman lafiya
2020-08-29 16:53:56        cri

A ranar Juma'a kwamitin sulhun MDD ya amince da kudirin dokar inganta tsarin shigar da mata ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Kudirin mai lamba 2538, ya bukaci mambobin kasashen MDD, da sakatariyar MDDr, da kungiyoyin shiyya da su kara kokarin da suke yi wajen samar da ingantacce kuma cikakken tsarin shigar da mata masu aikin tsaro da mata fararen hula cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya a dukkan matakai kuma a dukkan matsayi, wanda ya kumshi har da manyan mukaman shugabanci.

Kwamitin ya kuma bukaci kasashen mambobin su kafa wasu dabaru da wasu matakan da za su kara yawan jami'an tsaro mata da za a tura su wuraren gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiyar.

Sannan an bukaci a samar da hadin gwiwa a tsakanin kasashen mambobin, da kuma tsakanin MDDr da kungiyoyin shiyya da na kananan yankuna domin kara shigar da mata tare da ba su damar taka rawar gani a shirin ayyukan wanzar da zaman lafiyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China