Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhun MDD ya tsawaita wa'adin aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia
2020-08-29 16:16:55        cri

A ranar Juma'a kwamitin sulhun MDD ya amince da kudirin dokar sabunta aikin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Somalia UNSOM, inda aka kara shekara guda, har zuwa ranar 31 ga watan Ogastan shekarar 2021.

Kudirin mai lamba 2540, wanda ya samu amincewar dukkan kasashe mambobin kwamitin 15, ya bukaci shirin na UNSOM ya kiyaye da kuma karfafa aikin da yake gudanarwa a dukkan jahohin dake kasar Somalia, bisa ga tsarin ka'idojin kwamitin sulhun MDDr domin samar da cikakken tsaro.

Kwamitin sulhun ya yaba da goyon bayan da gwamnatin kasar Somalia ke baiwa shirin wanzar da zaman lafiyar na UNSOM, musamman game da shirin raya ci gaban siyasa da shirye-shiryen zabukan kasar na shekarar 2021, da shirin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar, da tattaunar sulhu, da kandagarkin tashe-tashen hankula, da inganta tsarin ayyukan 'yan sandan gwamnatin tarayya, da karfafa dokokin kasa, da yin garambawul a tsarin wanzar da zaman lafiya da tsaron kasar, da kyautata ayyukan yaki da rashawa.

Ya bukaci hukumomin kasar Somalia su samar da wani yanayin siyasa da na tsaro, domin samun damar gudanar da manyan zabukan kasar Somalia a duk fadin kasar kuma a dukkan matakai cikin nasara domin baiwa kowa damarsa ba tare da take hakkin wata jam'iyya ba, da kuma yin Allah wadai da duk wasu kalamai na batanci ko maganganun da za su haifar da tashin hankali a kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China