Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana kan gaba a fannin gudanar da gasannin wasan kwamfuta
2020-09-10 11:00:53        cri

 

Kamfanin nazarin yanayin tattalin arziki na Pricewaterhouse Coopers, ko kuma PwC, ya gabatar da wani rahoto dangane da sana'o'i masu alaka da ayyukan nishadi da watsa labaru a kwanan baya, inda ya ce a shekarar 2019, kasar Sin ta wuce kasar Koriya ta Kudu, da kasar Amurka, inda ta zama kasuwa mafi girma a fannin gudanar da gasannin wasan kwamfuta, wato na'ura mai kwakwalwa. Sa'an nan ya zuwa shekarar 2024 kasar za ta samu kudin shiga da ya kai dalar Amurka miliyan 670, ta hanyar gudanar da wannan sha'ani.

A cewar Mo Bin, wani jami'i a kamfanin PwC, yadda aka gudanar da wasu manyan gasannin wasan kwamfuta cikin nasara a kasar Sin, ya nuna yadda jama'ar kasar ke kara rungumar wannan wasa, don haka jami'in na kyautata zaton cewa, a nan gaba kasar ta Sin za ta ci gaba da rike matsayinta na kasuwa mafi girma a fuskar gasar wasan kwamfuta. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China