![]() |
|
2020-08-31 20:25:33 cri |
Da ma ba dukkan makiyaya daga garin tsaunin Tanggula suka kaura zuwa sabon kauyen. Har yanzu wasu na zama a tsaunin. Amma suna kiwon dabbobin gida bisa ka'idojin da aka tsara don kiyaye muhalli. Suna kokarin bullo da wani tsarin kiwon dabbobin gida, sayar da su da kuma sarrafa namansu baki daya.
Wadanda ke zaune a sabon kauyen fa? A shekarar 2011, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufar ba da kudin alawus ta fuskar kiyaye muhallin halittu a filin ciyayi. Yanzu 'yan kauyen Changjiangyuan ba su damu da harkokin kudi a rayuwa ba. Suna tafiya daidai da ci gaban birane. Wasu matasa kuma sun fara habaka ciniki a birane bisa ga kwarewarsu.
Har ila yau an kafa wata makaranta a kauyen na Changjiangyuan, inda malamai kwararru suke koyar da kananan yara yadda ya kamata. Wadannan makiyaya wadanda suka kaura zuwa sabon kauyen na ganin cewa, ilmantar da 'ya'yansu, ba su damar zuwa sauran wurare, da kara sanin abubuwan da ba su sani ba, hanya ce mafi dacewa wajen fito daga kangin talauci.
Kauyen Changjiangyuan ya riga ya cimma burin fito daga talauci. Yanzu 'yan kauyen suna kokarin bunkasa sana'o'i daban daban, a kokarin kara kyautata zaman rayuwarsu. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China