![]() |
|
2020-09-03 20:26:47 cri |
Akwai tuddai da kwari a unguwar Shengdi. Mazauna wurin suna zama a wani wuri maras fadi a cikin tuddai. Kwamitin kula da harkokin unguwar da kuma kungiyar da aka tura zuwa kauyen sun yi nazari kan halin musamman na yanayin kasa a wurin. Inda suka taimaka wa masu fama da kangin talauci raya sana'ar kiwon dabbobi. Ya zuwa watan Disamban shekarar 2019 da ta wuce, an fitar da dukkan mutanen dake unguwar daga kangin talauci.
Mahukuntan unguwar Shengdi sun yi amfani da halin musamman na unguwar, da fifikon da ake da shi a wurin, inda suka kara raya sana'ar kiwon dabbobi, lamarin da ya kara yawan kudin shiga da masu fama da talauci suke samu, tare da karfafa musu gwiwar samun wadata ta hanyar yin aikin tukuru da fita daga kangin talauci. Wadanda a baya suka yi fama da wahalar talauci sun yi aiki tukuru, suka kuma kara kokarin da suke yi don kyautata rayuwarsu, yanzu suna jin dadin zamansu rayuwarsu. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China