Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yabawa zaben da ya gudana a Misurata na kasar Libya
2020-09-05 17:42:53        cri
Tawagar musamman da MDD ta turo kasar Libya (UNSMIL), ta sanar da wani sako a jiya Juma'a don nuna yabo ga zaben da ya gudana cikin nasara a birnin Misurata na kasar Libya, wanda ya kasance wasu kilomita 200 a gabashin birnin Tripoli.

A cikin wannan sako, tawagar UNSMIL ta taya murnar jama'ar birnin Misurata kan yadda suka gudanar da wannan zabe a ranar 3 ga watan Satumban, cikin nasara, ba tare da gamuwa da wata matsala ba.

Tawagar ta kara da cewa, wannan zaben ya sake shaidawa mutanen duniya cikakkiyar niyyar jama'ar kasar Libya, kan yin amfani da hakkinsu na dimokuradiya, don zabar mutanen da za su wakilce su, duk da cewa birnin nasu da kasarsu na ci gaba da fuskantar wasu manyan kalobaloli masu yawa.

Stephanie Williams, wanda shi ne jami'in dake wakiltar babban sakataren MDD a kasar Libya, kana shugaban tawagar UNSMIL, ya bayar da wannan sanarwa a madadin tawagarsa, tare da yin kira ga jama'ar kasar Libya, da su yi rajista, sa'an nan ya ce ya kamata dukkan jama'ar kasar Libya su kara yin rajista da halartar irin wannan zabe da za a gudanar a nan gaba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China