Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin MMD sun yi kira da a dakatar da bude wuta a Libya
2020-05-14 15:34:24        cri

Jiya Laraba, mataimakin sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai na MDD, da hukuma mai kula da mahaurata ta kasa da kasa, da kuma WHO da dai sauran hukumomin majalisar, sun ba da wata hadaddiyar sanarwa, inda aka nuna cewa, rikicin da ya kara tsananta da kuma barkewar annobar cutar COVID-19 sun kawo babbar barazana ga jama'ar Libya.

Sanarwar ta nuna cewa, cikin shekaru 9 da aka samu barkewar rikici a kasarsu, 'yan Libya kimanin dubu 400 sun rasa gidajensu. Ban da wannan kuma, sanarwar ta ce, kungiyoyin kasa da kasa suna goyon bayan kiran da babban magatakardan MDD ya yi, game da tsakaita bude wuta a kasar, bisa dalilin jin kai, don kubutar da rayukan jama'a, ta yadda mahukuntan Libya, da abokanta za su iya tinkarar yaduwar COVID-19 yadda ya kamata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China