Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar AL ta nemi a tsagaita bude wuta a Libya
2020-04-05 17:16:15        cri
Kafofin watsa labaru na kasar Masar sun ruwaito a jiya Asabar cewa, babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa AL, Ahmed Aboul Gheit ya sake yin kira a kwanan baya, inda ya nemi a tsagaita bude wuta a dukkan wuraren dake cikin harabar kasar Libya baki daya, musamman ma a dakatar da taho mu gama da ake yi tsakanin sojojin manyan bangarorin kasar 2, a birnin Tripoli, hedkwatar kasar.

A cewar Gheit, dole ne a haramta yin amfani da bindigogi a wasu wuraren da ake rikici, da Larabawa suke zaune, ta yadda za a samu damar mayar da hankali kan aikin dakile yaduwar cutar COVID-19, da magance illar da annobar ka iya haifarwa al'ummu da hukumomin lafiya.

Gheit ya kara yin kira ga shugabannin bangarorin kasar Libya, da su dora muhimmanci kan moriyar kasa, da magance tsanantar yanayin rikici bisa shawarwarin da aka gabatar yayin muhawarar da MDD ta jagoranta. Daga bisani a yi kokarin wanzar da tsagaita bude wuta, don samun zaman lafiya mai dorewa a kasar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China