Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Libya dake gabashin kasar za su tsakaita wuta a lokacin Ramadan
2020-04-30 15:41:29        cri
Rundunar sojojin Libya dake da sansani a gabashin kasar ta sanar a ranar Laraba cewa, sojojinta za su tsakaita bude wuta a lokacin azumin watan Ramadan.

Sanarwar ta ce, "A wannan lokaci mai albarka, bisa kiraye kirayen da 'yan uwa da aminai suka yi daga kasashen duniya, inda suka nemi a kawo karshen yakin da ake yi a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma, babban kwamandan dakarun sojojin ya sanar da aniyar sojojin game da shirin tsakaita bude wutar, kuma za'a gaggauta aiwatar da shirin tsakaita bude wutar don dakatar da kai hare haren da mayakan sojojin ke kaddamarwa kan dakarun sojojin gwamnatin kasar dake samun goyon bayan MDD."

Kawo yanzu gwamnatin mai samun goyon bayan MDD ba ta ce uffan ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China