2020-09-04 14:47:20 cri |
Mataimakin magajin garin birnin Beijing Yang Jinbai ya bayyana cewa, a wannan karo, za a gudanar da taron kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa, da dandalin tattaunawar shugabanni guda hudu, da tarukan tattauna sana'o'in ba da hidima da kuma tarukan kwararru sama da guda 100, da sauran aikace-aikace da dama.
Haka kuma, ya ce, bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na bana ya hada harkokin bikin baje kolin al'adu, da na bikin baje kolin yawon shakatawa, da sha'anin kudi, da wasannin Olympics na lokacin sanyi, da na mutum-mutumin, da sauransu.
A sa'i daya kuma, za a gudanar da taro a fili da kuma ta kafar bidiyo, ta yadda mahalarta taron da 'yan kasuwan kasashen ketare za su halarci taron ba tare da wata matsala ba. Galibin mahalarta taron dake kasar Sin za su halarci tarukan da abin ya shafa da kansu, kana, ban da wasu dandalin nune-nunan da aka kafa cikin dakuna, an kuma kafa wasu dandalin nune-nune a fili. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China