Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar kasuwanci: karfin cinikin ba da hidima na Sin ya kai CNY biliyan 2200 cikin farkon watanni shida a bana
2020-08-05 11:13:40        cri

Rahoton da ma'aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin ta fidda a jiya Talata na nuni cewa, cikin farkon watanni shida na bana, gaba daya, karfin cinikin ba da hidima na kasar ya kai CNY biliyan 2200, adadin da ya ragu da 14.7% idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Dalilin raguwar adadin shi ne, raguwar tafiye-tafiyen mutane tsakanin wurare daban daban, sakamakon yaduwar cutar COVID-19.

Jami'in ma'aikatar kasuwanci ya bayyana cewa, raguwar cinikin ba da hidimar yawon shakatawa shi ne babban dalilin da ya haddasa raguwar, ban da wannan, aikin ba da hidima a fannin shigowa da fitar da kayayyaki na Sin cikin farkon watanni shida na bana, ya karu da 2.1%. Misali, aikin ba da hidimar shigowa da fitarwa a fannin fasahohi ya karu da 9.2%, adadin da ya kai 43.7% cikin aikin ba da hidimar shigowa da fitarwa na Sin.

Bugu da kari, an ce, a watan Satumban bana, za a gudanar da taron cinikin ba da hidima tsakanin kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020 a birnin Beijing, da kuma ta kafar bidiyo. Kuma babban taken taron bana shi ne "ba da hidima ga kasa da kasa, domin cimma moriyar juna", a lokacin, za a gudanar da taron kolin tattaunawar ba da hidimar kasa da kasa, da dandalin tattaunawar shugabanni, da taron karawa juna sani tsakanin masanan da abin ya shafa, da kuma bikin nune-nune da sauran aikace-aikace gaba daya iri 7, wadanda za su shafi fannoni da dama, kamar su fasahar 5G, da kuma fasahar kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam AI da dai sauran makamantansu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China